Kasuwanci
Buhari ya rufe matatun mai hudu na kasar nan – NNPC
Shugaban kamfanin mai na kasa NNPC Mele Kyari yace gwamnatin tarayya ta Rufe Matattun man kasar nan saboda rashin gudanar da ayyukansu yanda ya kamata.
Shugaban kamfanin ya bayyana hakan ne a yayin da yake tattauna da gidan talabijin na Channel’s a jiya laraba.
Mele Kyari ya ce an rufe matattun da suka hadar da na fatakwal da Warri da kuma na jihar Kaduna sakamakon yanda suke fitar da man ba bisa ka’idar da aka tsara tun da fari.
A cewar sa kamata yayi kowace matatar mai daya ta rika fitar da akalla kaso Casa’in sai dai kowace kan iya fitar da kaso sitin ne Kacal.
You must be logged in to post a comment Login