Manyan Labarai
Buhari ya shigo da masu rike da sarautun gargajiya wajen inganta tsaro-Sarkin Alkalman Kano
An shawarci gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, da ta shigo da masu rike da mukaman gargajiya da sarakunan musulunci wajen magance matsalar tsaro data dabaibaye kasar nan.
Sarkin Alkalman Kano Alhaji Ilyasu Labaran Daneji, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a zantawa ta musamman da ya yi dasu danagen da matsalolin tsaro da kasar ke fama dashi.
Sarkin Alkalman, ya ce a shekarun da suka shudea baya irin wannan tsarin aake dashi a kauyuka da birane , wanda a halin yanzu anyi watsi da tsarin , duba da haka akwai bukatar dawo da tsarin don magance matsalar tsaro musamman da tafi addabar yankin Arewacin kasar nan.
Labarai masu alaka.
Anyi kira ga shugaba Buhari da ya kawo karshen matsalar tsaro
Rundunar Sojin Najeriya za ta hada kai da Mafarauta da yan Vigilante don inganta tsaro
Alhaji Ilyasu Labaran Daneji ya kara dacewa hakan zai taimaka kwarai wajen inganta tsaro kasancewar masu rike da mukamai na gargajiya da sarakunan musulunci sun fi kusanci da talakawa don haka su zasu fi sanin matsalolin dake addabar su akan lokaci.
Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa, wakilin mu da ya halarci taron ya ruwaito cewar Sarkin Alkalman Kano, ya yi kira da al’ummar kasar nan da su addu’oin dqa kuma daukan matakan kare kai daga cutar nan ta Corona virus ami lakabin Covid-19 , duba da yadda da cutar ke cigaba da yaduwa a kasashen duniya.
You must be logged in to post a comment Login