Labarai
Buhari ya yi babban rashin aminin sa
Bayan da Allah ya yi masa rasuwa a jiya Litinin tsohon minista a jamhuriya ta biyu Malam Isma’ila Isa Funtuwa a Abuja yana da shekaru 78, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana rasuwar a matsayin babbar rashi.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa game da rasuwar daya daga cikin abokansa, malam Isma’ila Isa Funtuwa.
Sai dai ba’a bayyana dalilinan rasuwar marigayi Malam Isma’ila Funtuwa ba, amma wata majiya ta ce, rasuwar ta sa ba zata rasa nasaba da bugun zuciya ba.
A cewar shugaba Buhari rasuwar Malam Ismaila Funtuwa ya bar babba gibi mai wuyar cikewa.
Hakan na cikin wata sanarwa ce mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu.
Sanarwar ta ruwaito shugaba Buhari na taya ‘yan uwa da abokan arziki da kuma al’ummar jihar Katsina game da wannan babbar rashi da su ka yi.
You must be logged in to post a comment Login