Labarai
Buhari zai biya kungiyon NASU da SSANU kudaden Ariya
Gwamnatin tarayya ta amince da biyan kudaden Ariya ga kungiyoyin Jami’oi ta NASU da kuma mambobin kungiyar ma’aikatan jami’oi ta SSANU.
Hakan na cikin wata sanarwa da Ofishin babban akanta na kasa Ahmad Idris ya fitar ga manema labarai a Jiya.
Ta cikin sanarwar ta bayyana cewa, tuni Gwamnati ta Tattara rahoton kudaden ariya na watannin Afirilun bara zuwa watan Junairun baya domin gabatar dashi ga Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya.
Sanawar ta ce bayan gabatar da Rahotani kuma Ma’aikatar Ilimi zata aike da Rahoton ga zuwa ga Mai’akatar kasafin kudi da Tsare Tsare.
Samar da dangantaka mai kyau a jami’o’i zai kawo cigaba – Adamu Adamu
Hukumar NYSC ta gargadi Hukumomin Jami’o’in Najeriya
Ofishin ya kuma kara da cewa, gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin da zai gudanar da bincike kan korafin da kungiyoyin ke yi kan tsarin biyan albashi na IPPIS domin dakile matsalar.
You must be logged in to post a comment Login