Kiwon Lafiya
BUK: da wasu hukumomi sun Sami tallafin naira miliyan 100 don bunkasa madatsan ruwa
Cibiyar nazari akan a yankunan kasashen dake fama da rashin dausayi na jami’ar Bayero dake nan Kano tare da hadin gwiwar cibiyar bincike kan iri na kasa da kasa da kuma hukumar dake da bincke kan sararin samaniya sun sami nasarar samun tallafi na Naira miliyan 100 daga shirin bunkasa noman rani da inganta Madatsun ruwa na gwamnatin tarayya,TRAMING, don yin bincike RAMING.
Shirin na TRAMING shirin ne na bankin duniya dake karkashin ma’aikatar ruwa na gwamnatin tarayya.
Manufar shirin shi ne inganrtta noman rani don karfafa manonan rani wajn bunkasa ayyukan su.
Jami’ar Bayero it ace a kan gaba wajen hadin gwiwa bayan da ta sanya hannun yarjejeniyar a ranar 7 ha watan Maris din nan da muke ciki