Labaran Wasanni
Burinmu mu zama na goma a duniyar kwallon kwando- Akhator
‘Yar wasan kungiyar kwallon Kwando ta kasa ta mata D’Tigress Evelyn Akhator, ta ce buga gasar wasannin motsa jiki na bazara wato Olympic shi ne babban burinta, tun bayan da ta fara wakiltar kungiyar a matsayin ‘yar wasa.
Akhator, ta kara da cewa burin tawagar ‘yan wasan kungiyar ne dukkan su na ganin cewar kungiyar ta zama tana daga cikin kungiyoyi goma mafi hazaka na duniya.
“Burin kowanne dan wasa ne zuwa gasar Olympic, don haka ne ma da munji an ambaci sunan Olympic, sai mu kara jin wani karsashi na musamman, wanda zuwa yanzu haka fatan mu shine aganin shekarar badi mai zuwa don wakiltar kasar mu, inji ‘yar wasan”.
Labarai masu alaka.
Tennis: Venus da Serena Williams da Sloane Stephens basu ne bakar fataba kawai
Hukumar NBBF za ta cigaba da gudanar da gasar kwallon Kwando duk da kai ta kara da aka yi
Akhator , ta kara dacewa a baya ba wanda ya yarda cewar zamu zama daya daga cikin kasashe 20, dake kan gaba a duniyar kwallon Kwando ta mata, sai gashi yanzu muna mataki na 14, wanda ba karamin cigaba bane duba da cewa kwallon Kwando a kasar nan bata kai yadda take da farin jini a kasar Senegal ba.
Hakan na da matukar muhimmanci kwarai da gaske, ya kuma fito da sunan kasar nan a idon duniya wajen kwallon Kwando ta duniya
You must be logged in to post a comment Login