Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

2022 World Cup: Najeriya za ta yi wasa a watan Mayu – FIFA

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta tabbatar da cewa kungiyar kwallon kafa Najeriya Super Eagles za ta fara wasan zagaye na biyu a wasan neman tikitin zuwa gasar cin kofin duniya da za a gudanar a Qatar na shekarar 2022 a ranar 31 ga watan Mayun shekara mai zuwa.

A baya dai an so a fara zagaye na biyu a wasannin neman tikitin zuwa gasar a wannan watan da muke ciki kafin daga bisani a dage zuwa shekara mai kamawa bisa tangardar da aka samu a harkokin kwallon kafa sakamakon ballewar cutar Corona.

A cewar FIFA, za kuma a kawo karshen wasannin zagayen na biyu a watan Satumbar shekarar 2021, yayin da kuma za a soma zagaye na uku daga ranar 8 zuwa 16 ga watan Nuwamba 2021.

Super Eagles na a cikin rukuni guda da Cape Verde da Central African Republic da kuma Liberia a zagayen na biyu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!