Labaran Wasanni
CAF: Kasashe 46 na bukatar Ahmad ya sake tsayawa takara
Shugaban hukumar kwallon kafa ta Afrika wato CAF Ahmad Ahmad na cigaba da samun goyon baya ga mafi yawancin shugabannin kungiyoyin kwallon kafa a kasashe da dama dake nahiyar ta Afrika wajen sake zaben sa don maimaita shugabanci hukumar.
Shugabannin kungiyoyi kwallon kafa na kasashe 46 a cikin 54 a nahiyar ta Afrika ne ke yin kira tare da bada goyon baya ga Ahmad da ya sake fitowa takarar neman shugabancin hukumar karo na biyu.
A yanzu haka dai Ahmad na rike da shugabancin hukumar tun a shekarar 2017, yayin da ya cigaba da samun goyon bayan kungiyoyin kasashe da dama wajen sake tsayawa takarar sai dai amma kawo yanzu bai fito ya bayyana matsayarsa ba.
Za dai a gudanar da zaben hukumar a watan Maris na shekara mai zuwa ta 2021, inda kuma a ranar 12 ga watan Nuwamba mai kamawa ne za a rufe karbar takardar masu neman takarar shugabancin hukumar.
Haka zalika, kasashe 46 a cikin 54 sunyi mubayi’a ga Ahmad yayin da sauran kasashen da babu sunayen su a cikin takardar mubayi’ar sun hada da Algeria da Botswana da Ivory Coast da Najeriya da Sierra Leone da Afrika ta kudu da Uganda da kuma Zimbabwe.
You must be logged in to post a comment Login