Labarai
CAF Women’s CL: An zabi alkalan wasa 5 daga Najeriya

Mukaddashiyar Daraktar Gasa a hukumar kwallon kafa ta Najeriya, Ruth David na daya daga cikin alkalan wasa 5 daga Najeriya da za su jagoranci wasannin share fagen gasar cin kofin zakarun Afirka ta mata.
Sauran jami’an sun hadar da: Felicia Okwugba da Yemisi Akintoye da Friday Mfon da kuma Promise Uwaeme.
Za dai a gudanar da wasanni daga ranar 15 zuwa 30 ga watan Yulin 2021 a birnin Abidjan dake kasar Cote d’Ivoire.
Kasashe shida da za su fafata a wasannin su ne Najeriya da Jamhoriyar Niger da Cote d’Ivoire da Ghana da Togo da kuma Burkina Faso.
You must be logged in to post a comment Login