Labaran Wasanni
CAF za ta tsayar da matsaya a kan wasannin Champions League
Masu ruwa da tsaki a harkokin kwallon kafa a Afrika za su yanke hukunci kan ci gaba da gasar Champions League da kuma gasar cin kofin kalubale na Afrika a wannan watan na Satumba da muke ciki a kasar Morocco duk da cutar COVID-19 da tayi kamari a yankin.
Kasar ta Morocco ce dai za ta karbi bakuncin zagaye na farko a wasan kusa da na karshe a gasar ta Champions League da kuma wasannin kungiyoyi hudun karshe da za su fafata a gasar cin kofin kalubale a wannan watan na Satumba.
Jami’an hukumar kwallon kafa ta Afrika na nuna damuwar su duba da yadda annobar COVID-19 ke ci gaba da yaduwa a kasar ta Morocco.
A kalla 12 daga cikin ‘yan wasan kungiyoyi 16 da suke fafatawa a gasar Botola Pro 1, wadanda a ka samu masu cutar Corona, lamarin da ya saka dole ‘yan wasa ke zama a Otel ko a sansanin wasa, maimakon komawa gida a duk lokacin da a ka gama kowane wasa.
Ana dai sa ran gudanar da wasannin cin kofin kalubalen ne a ranar 22 ga wannan watan. Inda kungiyar Hassania Agadir ta kasar Morocco za ta kara da Renaissance Berkane ita kuwa Pyramids ta kasar Masar za ta kece raini da Horoya ta kasar Guinea.
You must be logged in to post a comment Login