Labaran Wasanni
CAS: Siasia ya nuna takaici bisa zan kafa da ake yiwa shari’ar sa
Tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles Samson Siasia, ya bayyana takaicin sa bisa jinkirin cigaba da sauraron shari’ar sa a kotun hukunta laifukan wasanni kan dakatar dashi daga shiga harkokin wasanni da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta yi.
An dai dage sauraron karar ne zuwa ranar 3 ga watan Fabrairun shekarar 2021, inda a baya aka tsaida ranar jiya Talata don cigaba da sauraron karar da Siasia ya daukaka.
Wannan shi ne karo na biyu da kotun ta dage sauraron karar sakamakon bullar cutar COVID-19 da tayi kamari a fadin duniya.
FIFA dai na zargin Siasia da laifin karbar cin hanci wajen canja jadawalin wasanni don amfanin masu caca a shekarar 2019.
Bayan haka ne hukumar ta FIFA ta dakatar dashi daga shiga harkokin wasanni har tsawon karshen rayuwar sa, yayin da ya ce bai aikata laifin da ake zargin sa dashi ba.
You must be logged in to post a comment Login