Labarai
PDP ta zargi gwamnatin Jigawa da rashin tabuka abun a zo a gani

Jam’iyyar PDP reshen jihar Jigawa, ta zargi gwamnatin jihar da rashin tabuka abun a zo a gani a sama da shekaru uku na mulkinta.
Shugaban kwamatin yakin neman zaben dan takarar gwamnan jihar ta Jigawa a Jam’iyyar PDP Alhaji Shehu Liman ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio.
Ya kuma ce, rashin ayyukan da gwamnatin Danmodi za ta nuna a Jihar ya sanya suke kiran rukuni na mutane, suna tarar ranakun kasuwa ana yin taruka da sunan nuna goyan baya ga gwamnatin.
Shehu Liman ya kuma ce tun da aka kafa gwamnatin jihar Jigawa ba a taba samun kudi daga gwamnatin tarayya ba sama da wannan lokaci amma Jam’iyyar APC bata gudanar da wani aiki na azo a gani ba.
Ya kuma ce al’ummar jihar Jigawa sun san abin da sukeyi babu wanda zai rudesu da wasu kudade kalilan domin a sauya musu ra’ayi.
Haka kuma, Alhaji Shehu Liman, ya kuma ce nan bada jimawa ba za su fara gudanar da yakin neman zaben dan takarar gwamnan na jihar jigawa a karkashin inuwar Jam’iyyar PDP Alhaji Mustafa Sule Lamido.
You must be logged in to post a comment Login