Kasuwanci
CBN ya musanta bada umarnin ci gaba da bayar da tsofaffin kudi a bankuna
Babban bankin Nijeriya CBN, ya ce, har yanzu bai bayar da umarni ga bankunan kasuwanci na su fara bayar da tsofaffin kudi ga kwastomomi ba.
Mai magana da yawun CBN Isa Abdulmumin, ne ya bayyana hakan a zantawarsa da jaridar Daily Trust.
Ya ce CBN bai bayar da wani sabon umarni ga bankunan kasuwanci ba kan hukuncin da kotun koli ta yanke a ranar Juma’ar da ta gabata na bayar da umarnin a rika rarraba tsofaffin takardun kudi ga abokan huldarsu ba.
A ranar juma’ar da ta gabata ne dai kotun kolin Nijeriya karkashin jagorancin mai shari’a Inyang Okoro, ta bayar da umarnin ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudin har zuwa ranar 31 ga watan Disamban bana.
You must be logged in to post a comment Login