Labaran Wasanni
Challenge Cup: Darma United ta yi rashin nasara a hannun Samba Kurna da ci 2-0

A ci gaba da gasar CHALLENGE CUP dake gudana a filin wasa na Mahaha Sports Complex da ke kofar Naisa a jihar Kano.
Wasan da aka buga yau Asabar 04 ga Satumba kungiyar kwallon kafa ta Darma United ta yi rashin nasara a hannun Samba Kurna da ci 2-0.
Za’a ci gaba da gasar a gobe Lahadi 5 ga Satumbar shekarar 2021.
Inda Dabo Babies za ta fafata da Dorayi Babba Lions a filin wasa na Diso United dake Mahaha Sports Complex a Unguwar Kofar Naisa.
Wasan mako na uku kenan da ake bugawa a gasar.
You must be logged in to post a comment Login