Labaran Wasanni
Champions league: Real Madrid ta doke Inter Milan da ci 1-0

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta doke Inter Milan da ci 1-0 a gasar cin kofin zakarun kungiyoyin kwallon kafa ta Turai Champions league.
An buga wasan ne a yau Laraba 15 ga watan Satumbar shekarar 2021.
Dan wasan Madrid Rodrygo ne ya ciwa kungiyar tasa ta Madrid kwallon a mintuna na 89 da wasan, bayan samun taimako da ya yi ta hannun dan wasa E-Camavinga.
Hakan ya sa aka tashi wasan da ci 1-0 bayn Kwashe mintuna 90 da Karin mintuna 2.
You must be logged in to post a comment Login