Labarai
Ci gaban Najeriya ba zai samu ba matukar ana amfani da tsohon tsarin zabe- Goodluck
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya ce ci gaban Najeriya ba zai samu yadda ya kamata ba, matukar ana ci gaba da amfani da tsohon tsarin zaben shugabanni wanda ya bayyana a matsayin wanda bai dace da zamani ba.
Goodluck Jonathan ya bayyana hakan ne yayin wani taro na tunawa da cika shekaru 162 da haihuwar fitaccen dan kishin kasa kuma jagoran fafutukar neman ‘yancin Najeriya, Herbert Macaulay.makole
Tsohon shugaban kasan ya ce, akwai bukatar Najeriya ta sauya tsarin zaben shugabanninta, tare da yin garambawul ga tsarin dimokuraɗiyyar kasar, domin samar da ingantaccen shugabanci da zai taimaka wajen cimma burin ci gaba.
Ya kuma yi gargadin cewa ci gaban kasar zai ci gaba da fuskantar tangarda idan har ba a sauya wannan tsarin ba.
You must be logged in to post a comment Login