Kiwon Lafiya
Cibiyar da ke dakile cututtuka ta kasa za ta karbi bakunci taron yaki da zazzabin lassa
Cibiyar dake dakile cututtuka ta kasa NCDC ta ce, ta shirya karbar bakuncin taron yaki da zazzabin Lassa ta kasa da kasa karo na farko a nan kasar.
Taron wanda za’a yi a tsakanin ranar 16 da 17 ga wannan watan na Janairu a babban birnin tarayya Abuja, mai taken ’’Shekaru 50 ana fama da cutar zazzabin Lassa, wanda hakan ya haifar da yawan kalubale’’ina mafita’’
Haka zalika taron zai tuna da cewar an kwashe shekaru 50 da gano cutar a nan Nageria, ana kuma kyautata zaton cewa masana da kararru a bangaren kiwon lafiya da kimiyya da suke aiki akan kwayar cutar tun daga gano ta kawo yanzu za su halaci taron daga ko’ina a fadin duniya.
Har’ila yau, masu gudanar da bincike daga kasashen duniya akan ita cutar zazzabin Lass za su yi tattauna da kuma samar da mafita wajen dakile cutar.
Babban jami’I a cibiyar dakile cututtuka ta kasa Chikwe Ihekweazu ya ce a halin yanzi Najeriya ce ke jagorantar shugabanci a yayin babban taron dakile cutar ta duniya.