Kiwon Lafiya
Cibiyar kare yaduwar cutuka ta kasa ta ce mutane 9 sun mutu sakamakon barkewar zazzabi a jihohi 7
Cibiyar kare yaduwar cututtuka ta kasa ta fitar da rahoton cewa akalla mutum 9 ne suka rasu sakamakon barkewar zazzabin shawara a kananan hukumomi 12 na Jihohi 7 na kasar nan a satin farko na wannan sabuwar shekara da muka shiga.
Jihohin su ne Kwara da Niger da Nassarawa da Kebbi da Kogi da Zamfara, da kuma nan Kano.
Baya ga wadannan Jihohi akwai wadanda suka sanar da barkewar zazzabin irin su Abia da Borno da Plateau da Enugu da Oyo da Anambra da Edo da Lagos da kuma Katsina.
Hukumar ta ce ya zuwa 2 ga Janairun nan mutum 358 suka kamu da zazzabin inda aka tura samfurin jinin mutum 230 zuwa dakunan gwajin jini guda 5 a cikin kasar nan, an samu tabbacin kamuwar mutum 63, sannan daga bisani aka tura zuwa dakin gwajin jini na hukumar lafiya ta Duniya WHO.