Kasuwanci
Cikin kankanin lokaci kamfanin facebook ya yi asarar dala biliyan 7- Mark Zuckerberg

Mamallakin Kamfanin facebook Mark Zuckerberg, ya samu tawaya a dukiyarsa da kimanin dalar Amurka biliyan bakwai.
Hakan ya biyo bayan rufe shafukan sada zumunta da aka yi na wasu awanni a ranar Litinin, lamarin da ya jefa sama mutum biliyan uku cikin takaici a fadin duniya.
Tunu dai babban jami’in Fasaha na kamfanin Facebook, Mike Schroepfe, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, suna neman gafarar duk masu amfanin da facebook bisa wannan matsala.
You must be logged in to post a comment Login