Kiwon Lafiya
Cikin watanni 2 kacal mun kwace miyagun kwayoyi da kudin su suka kai naira biliyan 60 – Buba Marwa
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta ce cikin watanni biyu da suka gabata, ta samu nasarar kwace miyagun kwayoyi daban-daban da kudin su suka kai naira biliyan sittin.
Shugaban hukumar Burgediya janar Buba Marwa mai ritaya ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a garin Ado Ekiti babban birnin jihar Ekiti.
Ya ce Najeriya a yanzu, babu babbar matsala da ta addabi jama’a fiye da ta’ammali da miyagun kwayoyi.
‘‘Ko da rashin tsaro da ke addabar kasar nan a yanzu, musamman ayyukan boko haram da ‘yan bindiga da ke satar mutane suna garkuwa da su, duk suna alaka da ta’ammali da miyagun kwayoyi’’
Matukar mun dauki matakai musamman ta bangaren dakile hanyoyin da miyagun kwayoyin ke shiga hannun jama’a, za a rage matsalar da akalla kaso hamsin cikin dari’’ a cewar Buba Marwa.
You must be logged in to post a comment Login