Labarai
Civil Defence ta kama jami’anta 3 da hannun kan mutuwar matasa a Neja

Hukumar Tsaron Fararen Hula ta kas, NSCDC ta kama tare da tsare karin jami’ai uku bisa zargin hannu a mutuwar wasu masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a jihar Neja.
Kakakin hukumar, Assistant Commandant Babawale Afolabi, ya bayyana cewa adadin jami’an da ke tsare yanzu ya kai 24, bayan da aka fara tsare jami’ai 21 sakamakon mutuwar mutanen da ke hannun hukumar.
Ya ce an mayar da dukkan jami’an da abin ya shafa zuwa shalkwatar hukumar da ke babban birnin tarayya Abuja, domin gudanar da bincike da kuma daukar matakin ladabtarwa.
A nasa bangaren, Kwamandan Janar na NSCDC, Ahmed Audi, ya ce duk jami’in da aka samu da hannu a lamarin zai fuskanci hukunci bisa doka.
You must be logged in to post a comment Login