Labarai
Hukumar NSCDC ta kama karin jami’ai 3 da ake zargi a mutuwar masu hakar ma’adinai a Neja

Hukumar Tsaro ta NSCDC ta kama tare da tsare karin jami’ai uku bisa zargin su da hannu a mutuwar wasu masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a jihar Neja.
Mai magana da yawun hukumar, AC Babawale Afolabi, ya bayyana cewa adadin jami’an da ke tsare yanzu ya kai 24, bayan da aka fara tsare jami’ai 21 sakamakon mutuwar mutanen da ke hannun hukumar.
Ya ce an mayar da dukkan jami’an da abin ya shafa zuwa shalkwatar hukumar da ke babban birnin tarayya Abuja, domin gudanar da bincike da kuma daukar matakin ladabtarwa.
A nasa bangaren, Kwamandan Janar na NSCDC, Ahmed Audi, ya ce duk jami’in da aka samu da hannu a lamarin zai fuskanci hukunci bisa doka.
You must be logged in to post a comment Login