Labarai
Gwamnatin tarayya ta dakatar da jami’an Civil Defence 20 kan zargin hannu a mutuwar mutane 37 a Neja

Gwamnatin tarayya ta dakatar da wasu jami’an rundunar tsaron farar hula wato “civil defence” ashirin, bisa zargin hannu a mutuwar mutane 37 a jihar Neja.
Mutanen dai na hannun jami’an rundunar ne bisa zargin hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, kafin daga bisani aka samu rahoton mutuwarsu.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya kuma sanar da kafa wani kwamitin bincike mai zaman kansa mai mambobi 10, domin gano ainihin abin da ya faru.
Ministan ya ce matakin ya biyo bayan umarnin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, na gudanar da bincike kan lamarin.
Ya ce jami’an da aka dakatar za su ci gaba da kasancewa cikin dakatarwar har zuwa lokacin da kwamitin zai kammala aikin sa.
Haka kuma, kwamandan NSCDC na jihar Neja shi ma yana cikin jami’an da aka dakatar tun farko.
Yanzu dai hankula na kan kwamitin binciken, wanda ake sa ran zai bayyana yadda mutanen 37 suka mutu da kuma irin rawar da jami’an rundunar suka taka.
You must be logged in to post a comment Login