Connect with us

Labaran Wasanni

Club Brugge: David Okereke ya kamu da Coronavirus

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Club Brugge, ta bayyana cewa dan wasan ta David Okereke dan asalin Najeriya, ya kamu da cutar Corona.

Club Brugge ta ce an samu dan wasan ne dauke da cutar, bayan da aka yi masa gwajin lafiya a kungiyar dake kasar Belgian.

David Okereke ya zama na uku a cikin manyan ‘yan wasan kasar nan da suka kamu da cutar bayan Paul Onuachu da Samuel Kalu.

Kungiyar ta kuma ce, an kilace dan wasan mai shekaru 23, haka kuma za’a sake yi masa gwajin a mako mai zuwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!