Kaduna
Corona: El-rufa’i ya bada damar buɗe ƙarin makarantu da Islamiyoyi
Gwamnatin jihar Kaduna ta amince da komawar sauran ɗalibai makaranta a ranar Litinin mai zuwa 22 ga watan Fabrairu, 2021.
Ɗaliban da za su koma makarantar sun haɗar da ƴan aji biyu na ƙaramar Sakandire da aji ɗaya da biyu na babbar Sakandare a makarantun kuɗi da na Gwamnati.
Sai kuma ɗaliban makarantun Firamare baki-ɗaya.
Haka kuma Gwamnan ya amince a koma makarantun Islamiyya a jihar daga ranar Litinin ɗin.
Hakan dai na cikin wata sanarwa da Kwamishinan ilimi na jihar Shehu Usman Muhammad ya fitar a daren Jumu’a.
Sanarwar ta nemi shugabannin makarantun da su shirya ci gaba da karatu a makarantu.
Sannan an nemi kowace makaranta kan ta tabbatar ta bi matakan kariya daga annobar Koronabairos.
Ma’aikatar ilimin ta ce, kwamitin yaƙi da cutar Korona zai sanya idanu domin tabbatar da cewa makarantun sun bi matakan.
Baya ga wannan ma’aikatar ilimin ta shawarci makarantun da su riƙa amfani da hanyoyin fasahar zamani wajen karatu.
Sannan za a ci gaba da karantar da ɗalibai ta hanyoyin rediyo da talabijin domin cike giɓin da aka samu.
You must be logged in to post a comment Login