Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

COVID -19 : Yawan masu dauke da cutar Corona ya haura dubu 67 a Najeriya

Published

on

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta sanar da karin sabbin mutane dari biyu da tamanin da daya da suka kamu da cutar corona a jiya Talata a nan Najeriya.

Hukumar na bayyana hakan ne, ta cikin rahoton da ta ke wallafawa a shafinta na Twitter a kowacce rana.

NCDC ta ce yanzu haka dai, adadin wadanda suka kamu da cutar a kasar nan ya kai dubu sittin da bakwai da dari takwas da talatin da takwas, sai dai a jiya jigar Legos ita ce da mafi yawan wadanda suka karu a jiya da adadinsu ya kai dari da talatin da uku.

Sai Abuja da ke da mutane 64 Kaduna na da 38 sai Imo da ke da mutum 15, sai jihar Rivers 11 Plateau na da 8 Ogun na da 5 Bayelsa da jihar Kwara na da 4 kowannen su.

Jihar Bauchi da Edo sun samu karin mutum 3 kowannensu, jihar Kano mutum 2 sai kuma Jihar Osun da ta samu karin mutum guda.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!