Coronavirus
CORONA: NYSC za ta kara sansanonin masu yiwa kasa hidima
Hukumar lura da masu yiwa kasa hidima (NYSC), ta ce nan gaba kadan za ta kara yawan sansanonin masu yiwa kasa hidima don daukar matakan kare kai daga kamuwa da cutar Corona da kuma harkokin tsaro.
Shugaban hukumar Birgediya Janar Shu’aibu Ibrahim ne ya bayyana haka a zantawar sa da manema labarai lokacin da ya kaddamar da bude sansanin ‘yan bautawa kasa rukunin A, zubi na biyu a Karu dake jihar Nassarawa.
Birgediya janar Shu’aibu Ibrahim, ya ce hukumar za ta cigaba da tuntubar hukumomin tsaro wajen bata shawarwari kan yadda za’a tsare lafiyar masu yiwa kasa hidima daga hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Shugaban ya kara da cewa ta hanyar hakan ne kawai za a tabbatar da kare lafiya da rayukan matasan ba tare da jefa su cikin hatsari ba, duba da matsalolin tsaro da wasu sassan kasar nan ke fama dashi.
You must be logged in to post a comment Login