Jigawa
CoronaWave2: Gwamna Badaru ya umarci ma’aikata su fara aiki daga gida saboda Corona
Gwamnatin jihar Jigawa ta umarci ma’aikata ƴan ƙasa da mataki na 12 su ci gaba da aiki daga gida saboda sake ɓarkewar annobar Korona.
Gwamnan jihar Muhammad Badaru Abubakar ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a ranar Laraba.
Gwamnan ya ce, umarnin zai fara daga ranar Alhamis 24 ga watan Disamban da muke ciki.
Sai dai ya ce, umarnin bai shafi ma’aikatan lafiya da na ma’aikatar kuɗi ba.
A makon da ya gabata ne gwamnatin jihar ta rufe makarantu saboda Korona.
You must be logged in to post a comment Login