Labaran Kano
Covid 19 a sanya dokar ta baci ga cutar-SEDSAC
Kungiyar bunkasa Ilimi da al’amurran jama’a da Dumukoradiyya SEDSAC, ta yi kira gwamnatoci a dukkanin matakai da su rubanya kokarin su wajen yaki tare da kawo karshen cutar Corona Virus, mai taken Covid 19, tare da sanya dokar ta baci akan lamarin don ganin an samu dai daiton al’amurra nan ba da dewa ba.
Shugaban kungiyar Kwamred Umar Hamisu Kofar Na’isa, ne ya yi wannan kiran a wata takarda da ya rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun sa.
Sanarwar ta kara dacewa rufe makarantu da ma’aikatu da kasuwanni, zai matukar kawo koma baya ga harkoki da dama musamman ma banagaren ilimi, don haka kungiyar ke kira ga gwamnatoci da su dau kwararan matakan cike gibin da ake samu a yanzu haka da sauran wasu bangarorin.
Labarai masu alaka.
Kungiyar kwadago ta bukaci a dau matakan Kariya na Corona
Covid-19: Kungiyar likitoci NMA ta raba kayan kare kai
Kungiyar ta SEDSAC, ta yi kira ga al’umma da subi matakai na kare kai da kuma bin dokoki sau da kafa da hukumomi suka gindaya tare da bin shawarwarin da likitoci da masu ruwa da tsaki akan harkokin lafiya,suka bayar a gefe daya kuma tare da killace kai don kaucewa yada cutar, kasancewar al’umma nda muhimmiyar rawa da zasu taka wajen takaita yaduwar wannan annoba.
Bugu da kari kungiyar ta yi kira da al’umma da su gudanar da addu’o’i da rokon Allah ya kawo karshen wannan annoba a kasar nan da duniya baki daya.
You must be logged in to post a comment Login