Manyan Labarai
Covid -19: Abi doka da shawarar ma’aikatan lafiya-Sarkin Zazzau
Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, ya yi kira ga al’ummar kasar Zazzau da jihar Kaduna gaba daya da su zama masu bin doka da oda, da karbar shawarwarin masana harkokin lafiya don kaucewa kamuwa da yaduwar Annobar Corona Virus.
Mai martaba Sarkin , ya yi kiran ne a yayin wata ganawa da ‘yan jaridu da kuma kira ga al’umma daya gudana a fadar sa yau dangane da halin da ake ciki na cutar mai lakabin Covid 19.
Alhaji Shehu Idris, yace yin hakan ya zama wajibi duba da yadda cutar ke kara yaduwa, wanda hakan ya sa tilas hukumomi da masu ruwa da tsaki su dauki matakan da suka kamata don ganin an gudu tare da tsira- tare.
Labarai masu alaka.
Covid-19: Maryam Abacha ta tallafawa mabukata da kayan abinci
Kyautatawa mabukata zai taimaka wajen ragi radadi- Sarkin Alkalman Kano
Sarkin ya kuma umarci al’umma dasu kai rahoton wanda suka ga yana da alamun cutar, in da ya kuma umarci Hakimai da dagatai da su umarci al’ummar su tsaftace muhallin su da jikin su.
Alhaji Shehu Idris Shehu, ya kuma yi kira ga limamai na Masallatai dana Coci, dasu umarci mabiyan su da sukara addu’a tare da kiyaye cunkusuwa waje daya don kaucewa yada cutar.
You must be logged in to post a comment Login