Coronavirus
COVID-19: An bude gidajen kallo a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta sahale a bude gidajen kallo kasancewar yana taimakawa wajen habaka tattalin arziki.
Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan a yau lokacin da yake ganawa da shugabannin kungiyar masu gidajen Kallo a fadar Gwamnatin Kano.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kuma yi kira a gare su dasu bi dukkan kaidojin cutar duba da yadda ake tara matasa a gidajen, a don haka ne ma ya basu safar baki da hanci dubu 40 domin rabawa a gidajen kallon nasu.
Covid-19: An gudanar da sallar Juma’a ta farko a jihar Kaduna
Ana cigaba da gwajin Corona gida-gida a Kano
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron da gwamna, shugaban kungiyar masu gidajen kallo na jihar Kano Sharu Rabiu Ahlan ya ce za su bi dukkan kaidojin cutar adon haka ne ma ya godewa gwamnatin ta Kano bisa wannan dama.
Wakiliyar mu Zahra’u Nasir ta ruwaito cewa kafin ganawa da kungiyar ma su gidajen kallon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki a jamiyyar APC da su kasance masu wayar dakan alummar su akan bin kaidojin cutar Corona yayin da yake zantawa da su a yau.
You must be logged in to post a comment Login