Coronavirus
Covid-19: An sassauta farashin kayan masarufi a Bauchi
Gwamnatin jihar Bauchi ta cimma matsaya da ‘yan kasuwar jihar kan sassauta farashin kayan masarufi domin saukakawa al’umma a wannan hali na yaki da Corona.
Cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar Bauchi ta fitar mai dauke da sa hannun mai taimakawa gwamnan jihar kan yada labarai Mukhtar Gidado tace anyi zama na musamman tsakanin kwamitin yaki da cutar Covid-19 a jihar da kuma bangarorin ‘yan kasuwar jihar inda aka cimma matsayar sassauta farashin kayan masarufi.
Kayayyakin da aka cimma matsaya akansu sun hada da, Shinkafa wadda za a rika sayar da buhu akan naira dubu goma sha bakwai da dari biyar (N17,500).
Sai Sukari wanda ya koma dubu goma sha bakwai (17,000).
Shi kuma Gero za a rika sayar dashi akan naira dubu goma sha biyu da dari biyar (N12,500).
Manja kuma naira dubu tara (N9,000).
Nama Kilo daya za a rika sayarwa naira dubu daya da dari biyu (N1,200).
Wannan ragin farashi dai zai fara nan take.
Karin labarai:
Covid-19: An saka “Lock Down” a kananan hukumomi 3 na jihar Bauchi
Da dumi-dumi Gwamnan jihar Bauchi ya kamu da COVID-19
You must be logged in to post a comment Login