Coronavirus
Tafidan Dakayyawa ya nemi Buhari ya sassauta dokar rufe Kano
Tafidan Dakayyawa Alhaji Imamu Tafida, ya ja hankalin al’umma da su kula tare da bin shawarwarin masana kiwon lafiya dangane da yanayin da ake ciki na annobar cutar Corona data mamayi al’ummar Duniya ciki har da nan Najeriya.
Alhaji Imamu Tafida, ya ja hankalin ne tare da yin kira, a wata hira ta musamman da Freedom Radio, a yunkurin da masu rike da sarautun gargajiya suke na taimakawa gwamnatoci a dukkan matakai a kokarin su na dakile yaduwar cutar Corona a cikin al’umma.
Basaraken, wanda Daya ne daga cikin Dattijawa kuma jagororin ‘yan kasuwar Abubakar Rimi, dake Sabongari, yace matakan da ma’aikatan lafiya ke dauka na yakar cutar, ya yi dai-dai da yadda tsarin addinin Islama ya koyar a addinance.
Alhaji Imamu Tafida, ya kara da cewa, masu sarautar gargajiya sun bada gagarumar gudunmowa, wajen taimakawa a wannan lokaci wajen wayar da kan al’umma, da shirye shiryen hukumomi na kwashe Almajirai zuwa garuruwan su.
Buhari ya rufe Kano ruf har zuwa mako biyu saboda Corona
Covid-19: Tawagar gwamnatin tarayya da za ta tallafawa jihar Kano ta iso
Buhari ya shirya yakar Corona a Kano
Ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni dasu tallafawa mabukata, da masu karamin karfi, tare da yin addu’o’in Allah ya kawo karshen wannan masifa.
Aminu Halilu T/Wada, wakilinmu ya ruwaito cewa, Basaraken ya kuma yi kira da babbar murya, ga shugaban kasa Muhammad Buhari tare da gwamna Abdullahi Umar Ganduje, da su saka baki wajen sasauta dokar da aka saka ta rufe gari na mako biyu, musamman ma a wasu kasuwannin da ake tasarifin kayan abinci.
You must be logged in to post a comment Login