Labarai
Covid-19: BUK ta umarci daliban dake zaune a makarantar su koma gidajen su
Jami’ar Bayero dake Kano ta umarci daliban da yanzu haka ke zaune a makarantar da su koma gidajen iyayen su, su zauna har nan da wata guda.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jami’ar Lamara Garba, ya fitar yau a madadin magatakardar jami’ar ta Bayero.
Haka kuma sanarwar tace daliban da suke zuwa daukar karatu daga gidajen su su dakata har zuwa lokacin da jami’ar za ta bukaci su dawo makaranta.
Sanarwar ta ce umarnin na zuwa ne bayan da ma’aikatar ilimi ta tarayya ta karkashin hukumar kula da jami’o’I ta kasa NUC, ta fitar da sanarwar cewa, Gwamnatin tarayya ta bada umarnin da’a rufe makarantun kasar nan ciki har da jami’o’i, sakamakon barazanar Cutar Corona.
Jami’ar ta ce umarnin zai fara aiki ne daga ranar litinin ashirin da uku ga watan maris din nan da muke ciki.
Ana kuma tsammanin ma’aikatan jami’ar za su ci gaba da gudanar da ayyukan su kamar yadda aka saba.
Sai dai ana shawaratar su da su kiyaye dukkan dokokin da masana kiwon lafiya ke bayarwa don gudun kamuwa da cutar covid-19.
You must be logged in to post a comment Login