Connect with us

Coronavirus

Adadin masu Corona ya doshi 3,000 a Najeriya

Published

on

Cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta kasa NCDC ta ce izuwa yanzu mutane 2,950 ne suka kamu da cutar Covid-19 a kasarnan.

A jadawalin wadanda suka kamu da cutar da cibiyar NCDC ta fitar a daren Talatarnan tace an samu karin mutane 148 da cutar ta kama a ranar Talatar.

Har ila yau, NCDC ta ce mutane 98 ne suka rasa ransu sanadiyyar cutar ta Corona a sassa daban-daban na kasarnan.

Sannan izuwa yanzu mutane 481 ne suka warke sarai daga cutar a Najeriya baki daya.

Karin labarai:

Covid-19: Gidauniyar BUA ta tallafawa Kano da kayayyaki na naira biliyan biyu

Adadin masu Corona ya kai 1107 a Legas

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!