Coronavirus
Covid-19: Gobe ranar sassauta dokar kulle a Kano
Gwamnatin jihar Kano tace gobe Alhamis za a sassauta dokar kulle da zaman gida a jihar kamar yadda aka saba domin baiwa al’umma damar sayen kayan abinci.
Maitaimakawa gwaman Kano na musamman kan yada labarai Salihu Tanko Yakasai ne ya bayyana hakan, a zantawarsa da wakilin mu Aminu Bello.
Salihu Yakasai na martani ne kan rahotonnin da ake yadawa cewa a ranar Alhamis babu sararawa saboda tsawaita dokar kulle da gwamnatin Kano tayi a ranar Litinin.
Labarai masu alaka:
Ganduje ya amince a rika bude mayankar “Abbatuwa” a ranakun sararawa
Ganduje ya kaddamar da rabon “Face Mask” miliyan biyu ga Kanawa
Idan zaku iya tunawa dai a kwanakin baya ne gwamnatin Kano ta amince da ranakun Litinin da Alhamis da karfe 10 na safe zuwa karfe 4 na yamma domin sararawa ga al’umma.
Tuni dai gwamatin ta Kano ta kaddamar da rabon amawalin rufe baki da hanci ga jama’a, bayan da ta sanya dokar tilasta amfani dashi a jihar domin dakile cutar Covid-19.
You must be logged in to post a comment Login