Coronavirus
Covid-19: Gwamnan Jigawa ya amince a gabatar da sallar idi
Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da ayi sallar idi a jihar amma banda mata da kana nan yara da kuma tsofaffi, yayin da suma mazaje majiya karfin da aka sahale suje sallar idin sai sun girmama tsarin bada tazara tsakanin juna, baya da amfani da abin rufe baki da hanci.
Gwamnan jihar Muhammad Badaru Abubakar ne ya bayya haka da yammacin ranar talatar nan a gidan gwamnatin jigawa dake Dutse.
Haka kuma Gwamna Badaru ya koka kan yadda korafi yayi yawa wajen yi wa dokar kulle da zaman gida karan tsaye, inda yace kan hakan ne gwamnatin jihar zata kafa kotunan tafi da gidanka, domin hukunta masu kin bin dokar.
Labarai masu alaka:
Covid-19: An baiwa gwamnatin Jigawa tallafin kayan abinci kan Corona
Za a tsaurara dokar kulle a Jigawa
Wakilinmu Muhd Aminu Umar Shuwajo ya rawaito Badaru na cewa gwamnatin jihar ta samar da gado 450 a cibiyoyin killace masu dauke da cutar.
Haka kuma ya kara da cewa duk mutanen dake son a bude su daga wannan doka ta zaman gida, tofa dole ne sai an gamsu da yadda suke bin doka sau da kafa kafin fatan su ya cika.
You must be logged in to post a comment Login