Addini
Covid-19 Gwamnatin Saudia zata bude ofishin Fasfo
Gwamnatin kasar Saudia, ta bude ofishin karbar fasfo a filin jirgin sama na Sarki Abdul Aziz, dake birnin Jeddah don shirin duba biza ta masu aikin Umarah.
Hakan ya biyo bayan tsare- tsaren da hukumomin a Saudia suke, na kammala aikin gyaran bizar wanda shaidar izinin zaman su a kasar ya kare tare da kara wa’adin zaman su a kasar ta Saudia, da wanda suka nemi bizar ta kafar sadarwa ‘internet’ a ofishin ma’aikatar aikin Hajji da Umara.
Rahotanni sun tabbatar da cewar, a wani umarni da masarautar kasar ta bayar, an cire sunayen wanda suka je yin aikin Umara, da suka wuce wa’adin da aka dibar musu, da wanda suke da matsaloli na kudade, daga cikin wanda za’a tuhuma, ko cin tarar su , daga cikin hadakar wanda kasar ta Saudia zata tisa keyar su zuwa kasashen su na Asali, sakamakon cewar sun samu tsaiko kasancewar bullar Cutar Corona Virus.
Labarai masu alaka.
Covid-19: Musulmai za su yi azumi kan Coronavirus
Covid-19: Al’ummar kasar nan su kwantar da hankalin su kan aikin Hajjin bana-Fakistan
Rahotannin sun kara da cewa ofishin fasfo din yace yin hakan na daga cikin umarni da kuma hadakar aiki tsakanin ma’aikatar aikin Hajjin kasar, da ma’aikatar Lafiya, da kuma ta harkokin jirgin sama, don dubawa da bibiyar hada- hadar shige da fice a cikin kasar , a gefe daya kuma tare da daukar matakan killace yaduwar cutar a fadin kasar.
You must be logged in to post a comment Login