Kiwon Lafiya
Covid-19: Kungiyar likitoci NMA ta raba kayan kare kai
Kungiyar Likitoci ta kasa reshen jihar Kano ta ce za ta ci gaba da aiki tukuru wajen ceto rayukan al’umma musamman a wannan lokacin da ake fama da cutar Corona a fadin Duniya.
Shugaban kungiyar Likitoci na kasa reshen jihar Kano Dakta Sanusi Muhammad Bala ne ya bayyana hakan yau yayin da yake mika kayayyakin kare kai ga membobin kungiyar da ke aiki a fadin asibitocin Jihar Kano.
Dakta Sanusi Muhammad Bala ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa da suka kara kudi akan yadda suke amfani dashi wajen kare rayukan al’umma a Asibitocin kasar nan dasu ji tsoron All- su sauko dasu yadda suke ada dan samun tsira anan duniya da kiyama.
Sanusi Muhammad ya kuma nuna takaicin sa bisa yadda a wannan lokacin kayayyakin kare lafiyar al’umma su kai tsada.
Ya kumaja hankalin ma’aikatan kiwon lafiya da su kasance a shirin kota kwana game da ayyukan su, ya kuma yi kira ga ma’aikatan lafiya a fannoni daban-daban dasu hade kansu wajen kare lafiyar Al’umma.
Kungiyar NMA dai ta raba Sinadarin wanke hannu wato hand Sanitizer guda tamanin da abin toshe hanci guda dubu hamsin ga asibitocin dake fadin jihar Kano dan kare lafiyar al’umma.
You must be logged in to post a comment Login