Coronavirus
Covid-19: Kungiyar tsaro ta Peace corp ta bada tallafi
Kungiyar samar da tsaro da tabbatar da zaman lafiya ta Peace Corp,reshen jihar Kano karkashin jagorancin babban kwamandanta Usman Abubakar Aliyu, ta gudanar da gangamin wayar da kai da bada kayan taimako na kariya da kamuwa daga cutar Corona Virus.
Kungiyar ta gudanar da gangamin ne a yau, tare da ziyartar kafafen yada labarai da suka hada da gidan Talabijin na NTA, Abubakar Rimi ARTV, da gidajen Rediyo Freedom da Rahmah, tare da raba musu kayan tallafi da za’a baiwa mabukata.
Kayan da kungiyar ta raba sun hada da Macroni, Magi da Omo, sinadarin tsaftace hannu sanitizer, da kuma takunkumin rufe hanci na facemask.
Labarai masu alaka.
Covid-19: Gwamnatin tarayya ta bada umarnin bayar da tallafi ga mabukata
Gwamnati tayi Adalci wajen rabon kayan tallafi-CITAD
Babban Kwamandan kungiyar,Usman Abubakar Aliyu, ya kara dacewa sunyi hakan ne don bada tasu gudunmowar ga al’umma duba da halin da aka shiga na wannan Annoba, ta Corona wadda ta addabi kasashen duniya, kuma ake jin labarin ta a wasu kasashe sai gashi yanzu ta shigo kasa har da jiha wanda zuwa yanzu haka har an samu mutuwar mutum daya, da kamuwar mutum 21.
Babban Kwamandan, ya kuma yi kira ga al’umma dasu baiwa hukumomi hadin kai tare dabin ka’idojin da ma’aikatan lafiya suka gindaya, don kaucewa kamuwa da yaduwar cutar.
Taron an karkare shi da rabawa wasu al’umma akan titi kayan wanke hannu da takunkumin sakawa a fuska, da safar hannu, da kuma zarcewa zuwa ziyartar wasu kafafen yada labaran na jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login