Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Gwamnati tayi Adalci wajen rabon kayan tallafi-CITAD

Published

on

Cibiyar fasahar sadarwa  da cigaban al’umma Citad, ta yabawa gwamnatin jihar Kano, wajen daukar matakan kare jihar bisa yaduwar Cutar Corona, ciki harda dakatar da zirga zirga wacce zata fara aiki a ranar Alhamis da karfe 10 na dare.

A wata sanarwa da jami’in fadakarwa da yada labarai ya sakawa hannu Ali Sabo aka kuma raba ga manema labarai, Cibiyar mai zaman kanta, ta ce la’akari da halin da ake ciki da kuma yadda cutar ke kara yaduwa , hakika yin hakan abin yabawa ne, sai dai kuma gwamnati tayi duba na tsanaki tare da fito da hanyoyin yin Adalci wajen tallafin da za a baiwa mabukata kasancewar jihar Kano, jiha ce mai dumbin al’umma wanda mafi akasarin su sai sun fita kullum suke samun abinda zasu ciyar da iyalan su.

Duba da haka, cibiyar ta ce yin hakan zai zamo anyi ba ayi ba, matukar ba a samar da kyakyawan tsarin da za’a kaucewa matsalolin da dumbin talakawan dake cikin jihar nan zasu fada ba, kasancewar saka dokar, don haka cibiyar ke kira ga gwamnati data fitar da tsari mai inganci da zai saukakawa al’umma mabukata a wannan lokacin.

Haka zalika sanarwar ta kara da kiran gwamnati ,data sanar da al’umma yadda  ake  ko ta raba dumbin kayan tallafi da kungiyoyi da masu hannu da shuni suka bayar, tare da jan hankalin gwamnatin tarayya wajen samar da kwamitin saka ido don tabbatar da anyi Adalci ba tare da an karkatar da kayan tallafin ba.

Sanarwar ta karkare da kiran masu hannu da shuni, da su taimaka wa marasa karfi a wannan lokaci da ake ciki a yankunan su .

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!