Labaran Wasanni
COVID-19: Osimhen zai koyi darasi a kuskuren da yayi – Gernot Rohr
Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Gernot Rohr, ya ce, dan wasan Najeriya dake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Napoli Victor Osimhen zai koyi darasi daga kuskuren da yayi na taka dokar kariya daga kamuwa da cutar Korona.
Osimhen dai ya kamu da cutar Korona yayin da ya koma kasar Italiya bayan da ya gudanar da taron murnar bikin haihuwarsa a nan gida Najeriya a watan Disambar shekarar 2020.
An samu faifan bidiyon dan wasan a tsakiyar mutane yayin gudanar da taron ba tare da ya saka takunkumin rufe baki da hanci ba a kafafen sada zumunta, lamarin da ya sanya kungiyarsa ta Napoli ta saka masa tara ta kudaden da ake biyansa na makwanni biyu.
A yayin tattaunawa da manema labarai, Rohr ya ce, “Wannan shine kuskuran da Osimhen yayi kuma babu shakka zai zamo darasi a rayuwarsa.”
You must be logged in to post a comment Login