Labarai
Covid-19: Sarkin Saudiya ya killace kansa
A kalla iyalan gidan Masarautar Saudiya 150 sun kamu da cutar Corona Virus da suka hada da gwamnan birnin Riyadh wanda yanzu haka ke kwance a sashen kula da marasa lafiyar da ke cikin matsanancin hali a asibiti, kamar yadda Jaridar New York Times ta Amurka ta rawaito.
Likitocin da ke kula da iyalan gidan sarautar sun samu takardar umarnin ware gadaje a kalla 500 a asibitin Sarki Faisal saboda yiwuwar samun karin mutane daga gidan sarautar dauke da cutar.
LABARAI MASU ALAKA
Covid-19 Gwamnatin Saudia zata bude ofishin Fasfo
Kasar Saudiya ta dakatar da zuwa Umara
An gargadi maniyyata guzurin ababan da aka hana a kasar Saudiya
Masarautar Saudiyar ta bai wa asibitin umarnin fitar da duk wani mara lafiyar da ke cikin matsanancin hali domin tanadar gadaje ga iyalan masarautar.
Rahotanni sun ce, yanzu haka Sarki Salman mai shekaru 84 ya kebe kansa a can wata fadarsa da ke kan tsibirin tekun Maliya a kusa da birnin Jeddah, yayin da Yarima Mai Jiran Gado, Mohammed bin Salman ya kwashi ministocinsa don komawa wani sashi na tsibirin, inda ya yi alkawarin gina sabon birni mai suna Neom.
You must be logged in to post a comment Login