Labaran Wasanni
COVID-19 Vaccine: Za a bai wa ‘yan wasan da zasu Tokyo Olympic 2020 kulawa ta musamman – Oladapo

Babban sakataren kwamitin Olympic na kasa Olabanji Oladapo, ya ce, za a bai wa ‘yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle da suka samu damar zuwa gasar Olympic ta 2020 da za a gudanar a birnin Tokyo dake kasar Japan, kulawa ta musamman idan an fara raba allurar rigakafin cutar Korona.
Za dai a dawo cigaba da gasar a ranar 23 ga watan Yuli mai zuwa bayan da aka dage gasar tsawon shekara guda sakamakon bullar cutar.
Rahotanni na kuma cewa, akwai alamun za a kara dage gasar duba da yadda cutar ta Korona ta kara kamari a wasu kasahe a duniya.
You must be logged in to post a comment Login