Coronavirus
COVID-19: Yadda al’ummar Karkara a jihar Kano ke zaman gida
A sakamkon dokar hana fita da gwamnatin Jihar Kano ta sanya don yaki da cutar Covid-19 na tsawon sati daya Freedom Radiyo ta ziyarci wasu garuruwan Karkara a nan Kano, don ganin yadda suka karbi dokar.
Alamu dai na nuni da cewa dokar ta yi tasiri a yankunan karkara fiye da yadda ake zato, bisa la’akari da yadda aka samu rashin fitowar jama’a tare da garkame shagunansu, musamman a garuruwan Doka da Rimin Gado.
Hakan ya sa muka tuntubi shugaban Karamar hukumar Alhaji Garba Shu’aibu Rimin Gado, don jin yadda lamarin ke kasancewa a karamar hukumarsa.
A garuruwan Kanye da Garo da kuma Kabo kuwa, suma dai an samu hadin jama’a wajen martaba dokar, duk da cewa an wasu shaguna kalilan da suka bude a Garo da kuma Kabo.
Alhaji Salisu Kabiru Kabo shi ne shugaban Karamar hukumar Kabo, ya shaida mana irin yadda mutane suka bi doka da oda kamar yadda ya kamata.
Covid-19: Gwamnatin tarayya ta bada umarnin bayar da tallafi ga mabukata
A ziyarar da wakilin namu yakai ya tarar da wasu gidajen mai a bude a kan titin Gwarzo, har ma muka ji ta bakin wani daga cikin masu sayar da man.
Freedom Radio ta lura da cewa an samu karancin zirga-zirgar motoci a yankunan da muka ziyarta, sai dai masu tafiya a kasa da kuma masu gudanar da bikin aure a garin Doka.
You must be logged in to post a comment Login