Kiwon Lafiya
Covid-19: Yadda masu zuba jari suka yi asarar biliyoyin kudi a Najeriya
Yayin da ake ci gaba da zaman fargaba sakamakon ci gaba da yaduwar cutar Corona, rahotanni sun ce, masu zuba jari sun yi asarar naira biliyan casa’in da tara a kasuwar hannayen jari na kasar nan cikin kwanaki biyu da suka gabata.
Jimillar jarin kasuwar wanda a ranar juma’ar da ta gabata yakai naira tiriliyan goma sha daya da biliyan dari takwas da arba’in da shida, an kammala hada-hada akan naira tiriliyan goma sha daya da biliyan dari bakwai da arba’in da bakwai.
Mun sake bunkasa cibiyoyin bincike kan cutar Covid 19
Covid-19: Buhari ya hana jami’an gwammati fita kasashen waje
Asarar dai ta fara tun a shekaran jiya litinin, lokacin da masu zuba jarin su ka yi asarar naira biliyan goma sha hudu, daga bisani lamarin ya kara ta’azzara a jiya talata, inda suka yi asarar naira biliyan tamanin da biyar.
Masana tattalin arziki dai sun ce farfagabar da ke zukatan masu zuba jari sakamakon ci gaba da gaba da yaduwar cutar Corona, ita ce babbar dalilin da ke kara ta’azzara lamarin.
You must be logged in to post a comment Login