Coronavirus
Covid-19: Yau za’a bude wuraren ibada a Nijar
Gwamnatin jamhuriyyar Nijar ta ce za a bude wuraren ibada daga yau Laraba 13 ga watan Mayu na shekarar 2020, bayan rufesu da akayi na tsawon lokaci domin dakile yaduwar cutar Corona.
Kakakin gwamnatin jamhuriyar Nijar ne ya bayyana cikin wani jawabi da yayi a gidan talabijin na kasar a daren ranar Talata.
Sai dai kakakin gwamnatin ya ce sun umarci dukkan gwamnonin kasar da shuwagabannin kananan hukumomin kan su sanya idanu sau da kafa domin ganin mutane sun yi biyayya ga matakkan da aka zayyana a wuraren ibadar.
Labarai masu alaka:
Covid-19: An sanya ranar komawa makarantu a Nijar
Gwamnan Katsina ya jagoranci tawagar haduwa da takwarorinsu na Kasar Nijar
A wani bangaren kuma gwamnatin ta dauki matakin cire dokar kulle da zaman gida a babban birnin Yamai.
Wakilin Freedom Radio a Nijar Yakuba Umaru Maigizawa ya rawaito cewa gwamnatin kasar ta ce ta dauki wannan mataki ne biyo bayan tattaunawa da shuwagabannin addinai da hukumomin kiwon lafiyar kasar.
You must be logged in to post a comment Login