Coronavirus
Covid-19: Za’a fara biyan ma’aikatan lafiya alawus-alawus dinsu
Gwamnatin tarayya ta ce cikin makon da muke ciki ne, za ta fara biyan ma’aikatan lafiya kudaden alawus-alawus din su na yakin da suke yi da Coronavirus da kuma sauran hakkokin su.
Gwamnatin tarayya ta kuma kara da cewa, ma’aikatan lafiyar zasu karbi kudaden na watannin Afrilu da Mayu kafin ranar Alhamis mai zuwa.
Ministan kwadago da nagartar aiki, Sanata Chris Ngige, ne ya bayyana hakan ga manema labarai, jim kadan bayan kammala wata ganawa ta musamman da shhugabannin kungiyoyin ma’aikatan lafiya a kasar nan.
Taron dai ya samu halartar Karamin ministan kwadago da nagartar aiki, Festus Keyamo da Akanta Janar na kasa Idris Ahmed da kuma karamin ministan Lafiya Olurunnimbe Mamora.
Yayin da su kuma kungiyoyin ma’aikatan Lafiyar suka hadar da shugaban kungiyar likitoci na kasa da na kungiyar likitoci masu neman kwarewa da kuma na hadaddiyyar kungiyar ma’aikatan lafiya ta Johesu.
Tun a cikin watan Afrilun da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kungiyoyin lafiya kan biyan su kudaden alawus-alawus din yaki da suke yi da cutar Covid-19 da kuma sauran hakkokin su.
You must be logged in to post a comment Login