Labaran Kano
Covid19: Gwamnatin Kano ta samar da lambobin kira kan Coronavirus
Gwamnatin jihar Kano ta samar da layukan waya biyar wadanda jama’a za su yi amfani da su, don neman daukin gaggawa da zaran sun ga wata alama da ke kamanceceniya da cutar Corona dama wasu cutittuka.
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba ya sanar a jiya.
Sanarwar ta ce, al’umma za su iya tuntubar Dr. Imam Wada Bello, daraktan kula da harkokin lafiyar jama’a da cutuutuka masu yaduwa ta kan wannan lambar waya 08050303343.
Sai Dr. Bashir Lawan Muhammad, daraktan magance cututtukan gaggawa na jihar Kano ta lambar waya 08099973292.
Da kuma Sulaiman Ilyasu, daraktan bibiyar cututtuka na jihar Kano ta lambar waya 08039704476.
Sai Mai kula da harkokin hukumar lafiya ta Duniya WHO a nan jihar Kano ta lambar 08037038597.
Sai kuma Yahaya Musa, Daraktan magance cututtuka a kan lambar waya 08176677497.
A cewar sanarwar, lambobin wayar da aka bayar don mutane su rika kira za su taimaka wajen dakile cututtuka dake yaduwa ga al’umma a wannan lokacin.
Haka kuma sanarwa ta bukaci al’umma da su yi amfani da hanyoyin da ma’aikatar lafiya da sauran ma’aikatu da hukumomin lafiya suka fitar don dakile yaduwar cutuka musamman cutar Corona.
Karin labarai:
Yadda cutar Corona ta shigo Najeriya
You must be logged in to post a comment Login