Labaran Wasanni
Cristiano Ronaldo na bikin cika shekaru 37
Gwarzan dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da kasar Portugal Cristiano Ronaldo na bikin cika shekaru 37 a duniya.
Cristiano Ronaldo dai an haifeshi a ranar 5 ga Fabrairun shekarar 1985 a garin Madeira da ke kasar Portugal.
Dan wasan dai cikakken sunansa shi ne Cristiano Ronaldo dos Santos Aveiro wanda kawo yanzu ya fafata a kungiyoyi da dama a duniya.
Cristiano Ronaldo dai ya fara bugawa kungiyar kwallon kafa ta Sporting Lisbon da ke Portugal a ranar daya ga watan Yulin shekarar 2002, inda ya zura kwallo 5 da taimakawa aka zura kwallo 6 a wasanni 31 da ya buga.
Sai daina a ranar 12 ga Agustan shekarar 2003 dan wasa ya koma Manchester United da ya samu nasarar zura kwallo 118 a wasanni 293.
Sai kuma a ranar shida ga Yulin 2009 dan wasan ya koma Real Madrid da ke kasar Spain.
Inda ya zura kwallaye 450 da taimakawa aka zura kwallaye 131 a wasanni 438 da ya fafata a kungiyar ta Real Madrid.
Kana a ranar 6 ga Yulin shekarar 2018 ya buga wasanni 135 ya zura kwallaye 101 har mada tai makawa aka zura kwallaye 26.
To amma a ranar 31 ga Agustan 2021 Ronaldo ya sake komawa Manchester United wanda zuwa yanzu ya zura kwallaye 24 da taimakawa aka zura kwallaye 3 a wasanni 24 da ya buga a kungiyar.
A kasarshi ta Portugal kuma ya zama dan wasa na farko da yafi kowa yawan zura kwallaye da jumulla 115 a wasanni 184.
Batun lashe gasa kuwa ya ci kofin zakarun turai Champions League har biyar a Real Madrid da Manchester United.
Ballon d’Or biyar
UEFA Super Cup uku.
Club World Cup hudu.
La Liga biyu.
Premier League uku.
Seria A biyu
FA Cup daya
Community Shield uku
Copas del Rey biyu
Spanish Super Cup biyu
Supercoppa Italia biyu.
Ga kasarshi ta Portugal kuma ya lashe gasar UEFA Nations League daya.
Gasar cin kofin kasashen turai ta UEFA European Championship daya
FIFA Confederations Cup daya.
Ya kuma lashe kyautuka kamar haka FIFA World Player.
Best FIFA Men’s Player.
Takalmin zinare na European Golden Shoe guda uku.
Sai kuma kyauta ta baya-bayanna da ya lashe itace FIFA The Best Special Award ta shekarar 2021.
Zuwa yanzu dai dan wasa Ronaldo abokin hamayyarsa shi ne Lionel Messi na kasar Argentina wanda a baya dan wasan Barcelona ne, a yanzu kuma yana tawagar PSG da ke kasar Faransa.
You must be logged in to post a comment Login